[gtranslate]
Mashhad, Meidane Shari'ati, kafin a ƙarasa layin Ahmad 1, Block na 15
Search

Jami'o'i mafi kyau a Iran

Jami’o’i mafi kyau a Iran

Loading

Zaɓaɓɓun Jami’o’in Ƙasar Iran

Jami’o’i mafi kyau a ƙasar Iran kan ba ma ɗaliban ƙasashen waje damar karatu tare da sanin mabambantan al’adun ƙasar. Duba da irin cigaban da Iran ta samu a ɓangaren karatu mai zurfi, ƙasar ta shiga sahun ƙasashen da ɗalibai ke rubibin zuwa karatu daga wurare daban-daban. Sanin jami’o’in na iya taimaka wa ɗalibai wurin zaɓen jami’ar da ta dace da su domin samun damar amfana da kayan aiki mafi inganci na ƙasar Iran.

Ƙasar Iran na da jami’o’i masu daraja da mabambantan fannoni, ta samar wa ɗalibai dama da yanayi mai kyau na karatu da samun gogewa a fagen kimiyya. Don haka ne muka yi ƙoƙarin tattaro muku wasu daga cikin jami’o’in a wannan rubutu namu. Ku kasance tare da mu.

Jami'o'in Iran

 

Tehran University

Jami’ar Tehran ɗaya ce daga cikin jami’o’in ƙasar mafi daɗewa kuma mafi daraja, an assasa ta a shekarar 1934. Ita ce jami’a mai daraja ta ɗaya a ƙasar Iran. Ana yin fannoni sama da 100 a cikinta irin su humanities, basic sciences, engineering, da medicine, tana daga cikin jami’o’in da suka dace da ɗaliban ƙasashen waje.

Keɓantattun Bayanai:

  • Jami’ar Tehran na da tsarin karatun ɗaliban ƙasashen waje a harshen farsi da turanci
  • Jami’ar ta tanadi muhalli da yanayi mai ƙara kuzari ta hanyar shirya tarukan tattaunawa da na al’adu
  • Ɗalibai na malaman jami’ar na wallafa maƙaloli masu inganci tsawon lokaci

Sharif University of Technology

An assasa jami’ar Sharif University of Technology a shekarar 1966, kuma tana cikin jami”o’i mafi inganci a ƙasar iran musamman a fannonin engineering da basic sciences. Ingancin ayyukanta na koyarwa da na bincike ya sanya ɗaliban ƙasashen waje rubibin zuwa wannan jami’ar karatu.

Keɓantattun Bayanai:

  • Jami’ar ta yi ƙarfi sosai a ɓangaren fannonin fasaha, fannoni irin su electrical engineering, mechanical engineering, da computer science. A baya-bayannan, jami’ar ta fara ƙosawa a fannonin nuclear.
  • Jami’ar fasaha ta Sharif ta yi tanadin kayan aiki na musamman domin gudanar da ayyukan binciken kimiyya, tare da bada ƙarfi a ɓangaren ƙirƙire-ƙirƙire.

Tehran University of Medical Sciences

Jami’ar Tehran University of Medical Sciences ɗaya ce daga cikin jami’o’in ƙasar Iran mafi nagarta a fagen kimiyyar likitanci da kiwon lafiya. Ita ma tana cikin jami’o’in da suka dace da ɗaliban ƙasashen waje masu son yin karatu a Iran duba da ingancin karatu da mabambantan fannoninta.

Keɓantattun Bayanai:

  • Jami’ar na bada damarmakin musamman ga ɗalibai ta hanyar asibitocin ta na koyarwa da kayan aiki na zamani
  • Tana da haɗin gwiwa da sauran fitattun jami’o’in duniya daga ƙasashe mabambanta

Amirkabir University of Technology

Amirkabir University of Technology (ana kuma kiran ta da Tehran Polytechnic), ita ma tana cikin sahun manyan jami’o’in Iran a fagen engineering da fasaha.

Keɓantattun Bayanai:

  • Jami’ar tana bada muhimmanci ga ayyukan bincike da projects na kimiyya.
  • Ɗaliban wannan jami’a na da damar musharaka a ayyukan bincike na ƙasa da ƙasa.

Shiraz University

Shiraz University na daga cikin manyan jami’o’in kudancin Iran. Ana yin fannoni masu yawa irin humanities, engineering, da basic sciences. Jami’ar Shiraz na cikin jami’o’in da ɗaliban ƙasashen waje ke burin zuwa karatu.

Keɓantattun Bayanai:

  • Jami’ar Shiraz na da manyan laburaruka da kayan aikin bincike, wanda hakan babbar damar karatu ce ga ɗalibai.
  • Jami’ar kan shirya taruka da bukukuwa na al’adu da na nishaɗi domin taimaka ma baƙin ɗalibai wajen samun sakewa a Iran.

Islamic Azad University

Ita ma tana cikin manyan jami’o’in firabet na ƙasar Iran kuma tana koyar da mabambantan fannonin karatu da kwasa-kwasai.

Keɓantattun Bayanai:

  • Tana da rassa sama da 400 a faɗin ƙasar Iran, kuma tana da mabambantan fannonin karatu.
  • Jami’ar na da haɗin gwiwa da wasu masana’antu, tana taimaka wa ɗaliban da ta yaye wajen samun aiki

Martabar Jami’o’in Iran a duniya

A shekarar 2004, jami’o’in ƙasar Iran sun taka rawar gani a mabambantan tsarukan ranking na duniya:

Tsarin Times: Jami’o’in Iran sun samu matsayi na 73 kuma sun yi fice a fannoni 10 daban-daban
Shanghai ARWU Ranking: 10 Iranian universities are ranked among the top 1000 universities worldwide, demonstrating their strong scientific research and international recognition.

Tsarin Shanghai ARWU: Jami’o’in Iran su 10 ne suka samu shiga sahun jami’a dubu na farko a duniya.

Tsarin QS: Jami’o’in Iran sun zo a matsayi na 7, kuma an ambace su a sahun manyan jami’o’in da suka fi jan hankali a duniya.

Tsarin Webometric: Cibiyoyi 440 daga ƙasar Iran suka samu shiga sahun jami’o’i 30,000 na duniya.

Zaɓaɓɓun Fannonin Karatu ga Ɗaliban Ƙasashen Waje

Akwai fannoni daban-daban waɗanda suka fi shahara ga ɗaliban ƙasashen waje saboda ingancin yanayin koyarda su da kuma kayan aiki da na bincike da za a amfana da su. Wasu daga ciki sun haɗa da: 

Fannonin Likitanci da Kiwon Lafiya:

Samun jami’o’i irin su Tehran University of Medical Sciences da Shahid Beheshti University of Medical Sciences, hankalin ɗaliban ƙasashen waje da yawa na karkata zuwa fannonin da suka shafi kiwon lafiya kamar medicine, dentistry, da pharmacy. Jami’o’in sun yi fice a tsarin karatu mai kyau da ingattatun kayan aiki na zamani.

Fannonin Engineering – Technology:

Kwasa-Kwasan engineering irin su electrical engineering, mechanical engineering, ko kuma computer engineering, sun yi fice a jami’o’i irin Sharif University of Technology, da Iran University of Science and Technology. Waɗannan fannonin na jan hankalin ɗalibai saboda yawan ayyukan yi masu alaƙa da su, da kuma maudu’an bincike masu zurfi.

Fannonin Humanities and Social Sciences:

Fannoni irin su history, sociology, da foreign languages na da jan hankali ga ɗaliban ƙasashen waje a makarantu irin su University of Tehran da Shiraz University. Fannonin na da alaƙa da tarihi da al’adun ƙasar Iran wanda hakan babbar dama ce ga ɗaliban da ke buƙatar zurfafa sani game da al’ummar ƙasar Iran.

Fannonin Basic Sciences:

Fannoni irin su physics, chemistry, da biology ma suna da farin jini ga ɗaliban waje musamman a jami’o’in da suka fi bada ƙarfi ga binciken ilimin kimiyya. Mafi yawan jami’o’in Iran na yin waɗannan kwasa-kwasan.

Fannonin Arts and Design:

Da yawan ɗalibai na sha’awar fannonin art, kuma jami’o’i irin Tehran University of Art, Isfahan University of Art, da Islamic Azad University na yin waɗannan kwasa-kwasan. Hakazalika, sauƙin kuɗin makaranta na jami’o’in Iran na cikin abubuwan da ke ƙasa jan hankalin ɗaliban ƙasashen waje zuwa yin karatu a Iran.

Related Posts
Leave a Reply

Your email address will not be published.Required fields are marked *