[gtranslate]
مشهد، میدان شریعتی، نرسیده به احمد آباد ۱، طبقه بالای بانک دی

Karatu a Jami'ar Arak

Karatu a Jami’ar Arak

Loading

Jami’ar Arak (University of Arak) ɗaya ce daga cikin manyan jami’o’in gwamnati wadda ke cikin garin Arak. Garin Arak kuma ɗaya ne daga cikin manyan garuruwan tsakiyar Iran kuma shi ne babban birnin lardin Markazi. Garin na da yanayi mai tsananin sanyi da iska mai danshi a lokacin sanyi da kuma busashsshen iska a lokacin zafi, akwai duwatsu a kewayen garin, tafkin Meighan da jejin Farahan duk abubuwa ne da suke da tasiri a yanayin garin.

Gabatarwa

Jami’ar Arak na daga cikin jami’o’i mafi kyau na Iran. Tana karɓar ɗalibai a kwasa-kwasai sama da 150 a duka matakan karatu. Yanzu haka jami’ar na da ɗalibai 7160 da malamai 521. Zuwa yanzu jami’ar ta wallafa maƙala 5102 a wallafe-wallafe da tarukan cikin gida.

Jami’ar Arak ta mallaki lambar yabo kuma ta wallafa mujalla 12 na musamman sannan ta shirya taruka 8 zuwa yanzu. Har ila yau jami’ar ta wallafa maƙala 6160 a matakin ƙasa da ƙasa. A shekarar 2023 da yawan maƙalolin da aka wallafa a wannan jami’ar suna ɗauke da kalmomin “SELF” da “virtual training” a matsayin muhimman kalmomin maƙala.

Wannan jami’a wadda a halin yanzu ita ce cibiyar koyarwa mafi girma da inganci a lardin, ta fara aiki ne a shekarar 1971 da sunan kwalejin kimiyya ta Arak a ƙarƙashin jami’ar Tarbiat Moalem ta Tehran. A shekarar 1989 ta zama jami’a mai zaman kanta inda ta ci gaba da aiki da suna Jami’ar Tarbiat Moalem ta Arak. An canja mata suna zuwa Jami’ar Arak ne a shekarar 1996 bayan an samar da tsarin bunƙasa ta da ƙara mata yawan makarantu da sabbin kwasa-kwasai.

Karatu a Jami'ar Arak

Martabar Jami’a

Tsarin ranking na QS ɗaya ne daga cikin tsarurrukan ranking ɗin jami’o’i na duniya wanda ƙungiyar “Quacquarelli Symonds” ta ƙasar England ke jagoranta. Tsarin na QS ya fara ranking ɗin jami’o’i tun daga shekarar 2010. A sakamakon da tsarin na QS ya fitar a shekarar 2023, jami’ar Arak ta zo a matsayi na 651 – 700 a tsakanin jami’o’i 760 na yankin Asia, ta kuma samu matsayi na 12 a tsakanin jami’o’in ƙasar Iran da suka samu shiga ranking ɗin.

A tsarin ranking na TIMES kuma jami’ar ta Arak ta samu matsayi na 1201+ a tsakanin jami’o’i 1600 daga ƙasashe 99 mabambanta na duniya. Haka kuma a tsakanin jami’o’i 58 na ƙasar Iran waɗanda tsarin na TIMES ya tantance, jami’ar Arak ta zo a matsayi na 46.

Har ila yau, jami’ar ta samu matsayi na 801 – 1000 a fannin engineering da technology (general engineering, electrical and electronic engineering, aerospace eng, civil eng, chemical eng). A ɓangaren physical science (mathematics and statistics, physics and astronomy, chemistry, geology, enviromental science, da soil science) kuma ta samu matsayi na 1001+.

Kuɗin makarantar jami’ar Arak

FacultyBachelor DegreeMaster DegreePhD
Human Sciences$300$500$800
Foreign Languages and Literatures$300$500$800
Basic Sciences$300$700$1,000
Engineering$400$700$1,000
Sport Sciences$400$750--
Agriculture and Natural Recourses$400$750--
Art$400----

Makarantu

Basic Sciences

Wannan kwalejin na nan a cikin babbar harabar jami’ar ta Arak. A kwalejin mai girman murabba’in mita 3800 inda ake yin kwas 11 a ƙarƙashin department 6, a matakin digiri, masters, da PhD akwai abubuwa irinsu ɗakin defense, ɗakin computer na ɗaliban masters da phd, azuzuwan karatu masu kayan kallo da sauraro, laboratory na psychology, studio da photolab. Bayan kammala ginin kwalejin sport science a Sardasht, department ɗin physical education ta koma can, kwalejin literature shi ma yana sardasht dukda cewa tsarin karatunsu da shugabancinsu ya bambanta.

Technical Engineering

Kwalejin Technical Engineering yana daga cikin sabbin makarantun da aka buɗe a jami’ar Arak a shekarar 2006 a harabar Sardasht, kodayake dama akwai kwalejin a wani wuri na haya kafin a kammala gina shi a wannan muhallin. Akwai department 7 a kwalejin tare da ingantattun kayan aiki da ɗakunan gwaje-gwaje.

Kwalejin ya fara aiki a wannan wuri mai girman murabba’in mita 11000 bayan karɓar izini a shekarar 2000, ya kuma baro tsohon muhallinsa na haya.

Makarantar Basic Sciences

Shi kuma kwalejin Basic Science ya baro tsohon muhallinsa na haya inda ya fara aiki a muhallinsa na yanzu mai girman murabba’in mita 12000 a shekarar 2002. A kwalejin akwai sassan koyarwa wato department guda 4 na mathematics, physics, chemistry, da biology da fannoni 7 a ƙarƙashinsu a matakin digiri, department 4 masu fannoni 24 a matakin masters, da kuma fannonin organic chemistry, mineral chemistry, physical chemistry, theoritical physics, solid state physics, fundamental particle physics, da kuma developmental cell biology. Kwalejin na ɗaukar ɗalibai a matakan karatu daban-daban kuma yana da ingantattun kayan aiki waɗanda suka keɓanci kowane department.

Economics and Administrative Sciences

An buɗe wannan makarantar a shekarar 2019 amma muhallinta ya jima sosai don kuwa akwai shi tun kusan lokacin da aka assasa jami’ar. Kwalejin ya fara aiki da kwasa-kwasan Law da Economics, amma a shekarar 2019 ne aka ƙara masa da kwas ɗin Industrial Management bayan amincewar majalisar ƙoli ta ma’aikatar ilimi.

Literature and Foreign Languages

A shekarar 2016 a wani zama na shuwagabannin jami’ar da kwamitin tafiyarwa na jami’ar, an tattauna yiwuwar samar da kwalejin literature inda aka amince da ƙudurin. Daga ƙarshe kwamitin zartarwa na jami’ar shi ma ya amince da samar da kwalejin na Literature. A halin yanzu wannan kwalejin yana da kusan ɗalibai 900 masu karatu a matakan karatu daban-daban.

Agriculture and Environment

An assasa wannan kwaleji a shekarar 2001 kuma yana da department 7 na koyarwa. Muhallin da wannan kwalejin take yanzu wuri ne mai kyau wanda kusan ya cika duka sharuɗa. A kwalejin akwai wani fili na gona mai girman hekta 160 wanda a nan ake yin ayyukan bita na noma, filin na jami’a ne amma tana ba mutanen gari haya na ɗan wani lokaci a kowace shekara.

Human Science

Wannan kwalejin na nan a cikin babbar harabar jami’ar ta Arak. A kwalejin mai girman murabba’in mita 3800 inda ake yin kwas 11 a ƙarƙashin department 6, a matakin digiri, masters, da PhD akwai abubuwa irinsu ɗakin defense, ɗakin computer na ɗaliban masters da phd, azuzuwan karatu masu kayan kallo da sauraro, laboratory na psychology, studio da photolab. Bayan kammala ginin kwalejin sport science a Sardasht, department ɗin physical education ta koma can, kwalejin literature shi ma yana sardasht dukda cewa tsarin karatunsu da shugabancinsu ya bambanta.

Sport Sciences

An assasa wannan kwaleji a shekarar 2017. Department ɗin physical education ya kasance a ƙarƙashin kwalejin human science har zuwa lokacin da aka assasa wannan kwaleji na sport science a Sardasht. Kwalejin na da abubuwa kamar zauren wasanni ɗauke da ingantattun kayan aiki, ana kuma gabatar da fannoni 3 a cikinsa

Art

A halin yanzu ana yin kwas 3 a wannan kwaleji na Art. Ɗaya daga cikin hadafofin jami’ar Arak na samar da wannan kwaleji shi ne mayar da hankali wajen bunƙasa fannonin fasaha (art) na cikin gida, na ƙasa da kasuwanci.

Karatu a Jami'ar Arak

Kwasa-Kwasai

  • Psychology (BSc), General Psychology (MSc)
  • Educational Sciences (BSc), Educational Technology (MSc)
  • Theology (BSc), Qur’an and Hadith Sciences (MSc, PhD)
  • Islamic Studies (BSc)
  • History (BSc), History of the Islamic Period (MSc)
  • Counseling (BSc)
  • Persian Language and Literature (BSc, MSc, PhD)
  • Arabic Language and Literature (BSc, Master’s, PhD)
  • English Language and Literature (BSc, MSc)
  • English Translator (BSc, MSc)
  • English language teaching (BSc, MSc)
  • Political Science (BSc)
  • Law (BA)
  • Economics (BSc)
  • Industrial Management (BSc)
  • Environment (BSc, MSc)
  • Medicinal and Aromatic Plants (associate, BSc, MSc)
  • Medicinal and Aromatic Plants (associate, BSc, MSc)
  • Water Engineering (BSc, MSc)
  • Agricultural Machinery (BSs, MSc)
  • Animal Science (BSc, MSc)
  • Biosystem Mechanical Engineering (BSc, MSc)
  • Chemical Engineering (BSc, MSc, PhD)
  • Civil Engineering (Bachelor’s, MSc)
  • Computer Engineering (Bachelor’s, MSc, PhD)
  • Power and Telecommunication Electrical Engineering (BSc) – Power and Control (MSc)
  • Mechanical Engineering (BSc, MSc)
  • Materials and Metallurgy Engineering (BSc, MSc)
  • Industrial Engineering (BSc)
  • Mathematics (BSc, MSc, PhD)
  • Physics (BSc, MSc, PhD)
  • Chemistry (BSc, MSc, PhD)
  • Biology (BSc, MSc, PhD)
  • Statistics (BSc)
  • Carpet (BA)
  • Handicrafts (BA)
  • Graphics (BA)
  • Cartography (BA)
  • Movement Behavior and Sports Psychology (Bsc, MSc)
  • Pathology and Physiology (BSc, MSc)
  • Sports Management (BSc and MSc)

Abubuwan More Rayuwa

Daga cikin abubuwan da jami’ar Arak take da akwai zauren wasanni, self na abinci, masallaci, koren fili, da sauransu. A kwalejin Human Science na jami’ar akwai zauren defense, ɗakin computer, azuzuwan kallo da saurare, laboratory na psychology, studio da photolab.

A kwalejin technical engineering akwai kayan aiki na musamman da ɗakunan gwaje-gwaje. A kwalejin basic science akwai gidan tarihi, plant herbarium, ɗakunan gwaje-gwaje na musamman ɗauke da kayan aiki na zamani, ɗakin computer, da keɓantaccen laburare.

Karatu a Jami'ar Arak

Wuraren kwana

  • Wurin kwana na Shahid Golamreza Rezayi (na maza) a harabar Sardasht (ya keɓanci ɗaliban engineering, sport science, da basic science)
  • Wurin kwana na Amirkabir (na maza) a harabar Arak (ya keɓanci ɗaliban agriculture, management science, economics, literature, da human science)
  • Wurin kwana na Al Zahra (na mata)

Yanayin Wuri

Jami’ar Arak na nan a unguwar Hefdah Dastgah a garin Arak, titin Taleghani, Daneshjo. A kusa da jami’ar akwai wurare kamar kemis na Helal Ahmar, Ale Ich Cafe, Pasaj Rouz, da Mo’allem Hotel.

Adireshi: Arak, Meidan Basij, Bolvare Karbala, University of Arak

Shafin jami’a: http://araku.ac.ir


Tambayoyi da ake yi game da jami’ar Arak

  1. Hostel nawa jami’ar Arak take da su?
    Wannan jami’a na da hostel masu yawa saboda yawan ɗalibanta. Za ku iya samun cikakken bayani a cikin rubutunmu.
  2. Wasu irin abubuwa jami’ar take da shi kuma minene alfanun karatu a jami’ar?
    Daga cikin fa’idojin da za ku samu na karatu a wannan jami’ar shi ne kayan aiki na zamani da take da su da kuma nasarorin da ta samu wanda mun ambace su a cikin wannan maƙalar.
  3. Makarantun wannan jami’a nawa kuma a wasu fannoni suke aiki?
    Jami’ar ta kasu kashi biyu sannan tana da makarantu 6, mun kawo fannonin a cikin rubutunmu.
Related Posts
Leave a Reply

Your email address will not be published.Required fields are marked *