Karatu a Jundishapur University of Medical Sciences da ke garin Ahwaz a matsayinta na ɗaya daga cikin cibiyoyin karatu masu tarihi kuma matakin da ta taka a ɓangaren ilimi abun lura ne sosai ga mutane. A wannan rubutun, mun maida hankali akan batun karatu a Jundishapur University of Medical Sciences, kayan aikinta, da sauransu.
Gabatarwa
A garin Ahwaz akwai fitattun jami’o’in Iran (domin ƙarin bayani kuna iya bincikar rubutun Karatu a garin Ahwaz) Misalin ɗaya daga cikin waɗannan cibiyoyin, ita ce Jundishapur University of Medical Sciences and Health Services Ahwaz wadda aka assasa a shekarar 1954. Saboda bunƙasar matsayinta na ilimi tun bayan assasa ta zuwa yanzu, ana kallon Jami’ar Ahwaz a matsayin jami’a mafi muhimmanci a kaf jami’o’in yankin Khuzestan.
A halin yanzu, akwai ɗalibai 6400 da malamai 646 a wannan jami’a. Bincike ya nuna cewa, wannan jami’a ta wallafa maƙalar ilimi guda 3521 a taruka da wallafe-wallafen cikin gida, da maƙaloli 9053 karɓaɓɓu a matakin ƙasa da ƙasa. Hakazalika ita ce mamallakiya kuma mawallafiyar mujalloli na musamman guda 6. Zuwa yanzu an gudanar da taruka 9 a cikin wannan jami’a.
Martabar Jami’a
Ahvaz Jundishapur Uiversity of Medical Sciences a karonta na farko wajen shiga tsarin ranking na Times shekarar 2022, ta yi nasarar samun matsayi na 601-800 kuma ta shiga sahun fitattun jami’o’i na duniya.
Makarantu
Bayan kafa makarantu daban-daban masu zaman kansu, adadin ɗaliban da ake karɓa a wannan jami’ar shima ya ƙaru.
_Makarantar Medicine
_Makarantar Public Health
_Makarantar Pharmacy
_Makarantar Rehabilitation
_Makarantar Allied Medical Sciences
_Makarantar Dentistry
_Makarantar Nursing & Midwifery
_Harabar Khodgardan
_Bustan Nursing College
Asibitoci
_Asibitin Shafa, Ahwaz
_Asibitin Baghaee2, Ahwaz
_Asibitin Razi, Ahwaz
_Asibitin Sinai, Karun
_Asibitin Abozar, Ahwaz
_Asibitin Salamat, Ahwaz
_Asibitin Golestan, Ahwaz
_Asibitin Imam Khomani, Ahwaz
_Asibitin Ayatollah Taleghani
Cibiyoyin Bincike
_Nanotechnology
_Cancer
_Hearing
_Toxicology
_Gastrointestinal infections
_Cardiovascular
_Environmental
_Research consultation
_Laboratory Animals
_Improving Reproductive Health
_Comprehensive Research Laboratory
_Infectious and Tropical Diseases
_Center for the Growth of Pharmaceutical Technologies
_Fertility and Infertility and Fetal Health
_Clinical Research Development Unit of Golestan Educational Center
_Physiology
_Gastrointestinal Infections
_Medicinal Plants
_Research Consultation
_Marine Pharmaceutical Sciences
_Comprehensive Research Laboratory
_Nutrition and Metabolic Diseases
_Hyperlipidemia Research Center
_Renal Insufficiency
_Diabetes
_Pain
_Cellular and Molecular
_Air Pollution
_Eye Infections
_Menopause and Andropause
_Thalassemia and Hemoglobinopathy
_Social Factors Affecting Health
_Musculoskeletal Rehabilitation
_Nursing Care in Chronic Diseases
Kwasa-Kwasan karatu
_General Practitioner
_Pharmacy
_Dentistry
_Surgery Room
_General Hygiene
_Obstetrics and Gynecology
_Urology
_Orthopedics
_Nursing
_Radiology Technology
_Audiologists
_Laboratory Sciences
_Nutritional Science
_Speech Therapy
_Midwifery
_Anesthesia
_Environmental Health Engineering
_Occupational Therapy
_Physiotherapy
_Glands
_Children
_Neurosurgery
_Anesthesia
_Medicinal Chemistry
_Oral and Maxillofacial Surgery
_Health Information Technology
Anesthesia
_Physiotherapy
_Audiology
_Medical Genetics
_Medical Entomology and Fight Against Vectors
_Clinical Pharmacy
_Management of Health Services
_Poisoning and Forensic Medicine
_Orthodontic
Da sauransu…
Domin ƙarin bayani, ku sauke list ɗin kwasa-kwasan Jundishapur University of Medical Sciences
Ɗakunan Karatu
_Laburaren School of Health
_Laburaren School of Nursing and Midwifery
_Laburaren Medical School
_Laburaren Paramedical school
_Laburaren Paramedical School
_Laburaren School of Pharmacy
_Laburaren School of Dentistry
_Laburaren Bostan Nursing School
_Laburaren Autonomous School
_Laburaren Asibitin Abuzar
_Laburaren Asibitin Imam Khomeini
_Laburaren Asibitin Razi
_Laburaren Asibitin Shahid Beqaei 2
_Laburaren Asibitin Taleghani
_Laburaren Asibitin Golestan
_Laburaren Digital
Abubuwan Alfahari
_Lashe matsayi na biyi a gasan Olympiad na ɗalibai a filin asibiti
_Lashe mastayi na farko a jarabawar kwamitin musamman na cututtuka masu yaɗuwa
_Samun matsayi na biyu a fannin ilimin ilimin cututtukan jini na yara
_Samun karɓuwar dukan ɗalibai a babbar jarabawar ƙasa da ƙasa
_Zaɓen cigaban karatu – Kwas ɗin Pharmacy a matsayin kwas ɗin online
Abubuwan more rayuwa
Bayan kammala karatunsu, ɗaliban Ahvaz Jundishapur University of Medical Sciences zasu iya yin attachment da internship ɗinsu a asibitoci da cibiyoyin jinya tare da sa idon Jundishapur University of Medical Sciences. Ɗaya daga cikin muhimma ayyukan Jundishapur University of Medical Sciences ga ɗalibai da kuma bunƙasa matakin ilimsu, shi ne samar musu da masana kuma ƙwararrun malamai.
Jundi Shapur University of Medical Sciences, kamar dai sauran jami’o’in, ta yi tanadin kammalallun wuraren kwanan ɗalibai ta fuskacin kayan aiki domin kulawa da lafiya da kuma walwalar su. Ɗalibai zasu iya amfani da waɗanna hostel dai-dai da matakin karatunsu, misali, ɗalibai masu karatun masters ko diploma zasu iya amfani da hostel na iya tsawon shekara 2 kawai, ɗaliban digiri kuma shekara 4, ɗaliban Medicine da Dental kuma iya shekara 6 kawai. List ɗin wuraren kwana:
_Wurin kwana na Bostan (na ɗalibai maza)
_Wurin kwanan Gholestan ( na ɗalibai mata)
_Wurin kwana na Shohada lamba 1 (na ɗalibai maza)
_Wurin kwana na Shohada lamba 3 (na ɗalibai maza)
Muhalli:
Jami’ar Jundishapur na nan kusa da Chamran University of Ahvaz and Farvardin, Dey, Randabawul na Shohada. Ta fuskar muhalli, tana kusa da wurare kamar Asibitin Golestan, Gidan tarihi na Ahvaz Science and Nature, Babban ginin Sazeman Markazi, Bankin Refahe Kargaran, Central Research Laboratory, Soma Fast Food Restaurant, Shahrake Barq, da kuma Tiara Restaurant.
Magana da Ahvaz Jundishapur University of Medical Sciences
Adireshi: Titin Golestan – Ahwaz -Iran
Tambayoyin da ake yawan yi
- Wasu irin takardu ake buƙata domin yin rajista a Jundishapur University of Medical Sciences?
Passport, hoto, script na results, Certificate, CV, Motivation letter, Recommendation letter. - Shin biyan kuɗin hostel wajibi ne?
Eh, biyan kuɗin hostel wajibi ne. - Shin zai yiwu ɗaliban Iraki su yi transfa daga Junsdishapur University of Medical Sciences?
Eh, ɗaliban Iraƙi zasu iya yin transfa zuwa ƙasarsu bayan sun kammala zango biyu na karatu.
[neshan-map id=”14″]